1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun EU ta soke tallafin ceto ga Lufthansa

Abdullahi Tanko Bala
May 10, 2023

Wata kotun tarayyar turai ta soke tallafin euro biliyan shida da hukumar tarayyar Turai a Brussels ta bai wa kamfanin zirga zirgar jiragen saman Jamus Lufthansa a lokacin annobar Corona.

https://p.dw.com/p/4RA97
Deutschland Frankfurt am Main Flughafen | Flugausfälle nach IT-Panne
Hoto: Arne Dedert/dpa/picture alliance

Kotun ta ce tun farko bai kamata hukumar tarayyar Turan ta amince da hukuncin da gwamnatin Jamus ta yanke na bai wa kamfaninn na Lufthansa tallafin ba.

A lokacin annobar Corona kasashen tarayyar Turai sun rika yin sassauci ga tsauraran dokokin EU na ba da tallafin ceto ga kamfanoni wanda ya sa hukumar tarayyar Turan ta amince da tallafin euro biliyan shida ga kamfanin Lufthansa a watan Junin 2020 wanda gwamnatin Jamus ke da hannun jarin kashi 20 cikin dari a cikinsa.

Kamfanonin jiragen sama na Ryanair da Condor Air suka shigar da karar inda suka ce an yi musu rashin adalci wajen ba da tallafin.