1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zanga-zangar neman sauyi a Sudan

Mahmud Yaya Azare SB
December 26, 2018

Jami'an tsaron Sudan na kara matsa kaimi wajen murkushe zanga-zangar neman sauyin da ke kara yin kamari a kasar yayin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke gargadin su yi hattara kar su wuce gona da iri.

https://p.dw.com/p/3AeQ2
Unruhen im Sudan - Proteste in Khartum
Hoto: Reuters/M.N. Abdallah

Jami'an tsaron Sudan sun tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Khartoum, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa fadar mulkin kasar da zimmar mika doguwar takaddar ga Shugaba Omar Hassan Albashir da ke zayyanamar dalilunsu na yimar kira da ya yi murabus.

Wata da akai wa rauni  daga cikin gamayyar kungiyoyin 'yan kwadagon da suka shiga zanga-zangar kasar ta ce, farmakin da jami'an tsaron suka kai musu da niyyar kisa ne. Wani daga cikin dubban matasa marasa aikin yi da ke kan gaba wajen zanga-zangar neman rage farashn burodin da ta rikide ta neman sauyin gwamnati, ya ce sun gaji da gafara san da Shugaba Albashir ya yi shekara da shekaru yana musu ba su ga kaho ba.

Sudan Khartum Bäckerei Brot
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Kungiyar Amnesty International da ta yi ikirarin cewa, kimanin mutane 37 jami'an tsaron Sudan suka halaka cikin tsukin mako guda, ta nemi da bai wa 'yan kasar hakkinsu na yin zanga-zangar lumana, tana mai gargadin mahukunta da yaba wa aya zaki idan har suka ci gaba da keta hakkin dan Adam.

Shugaba Albashir dai, wanda ya bayyana gaban dandazon magoya bayansa a jihar Aljazeerah, don karyata rade-radin da ke cewa, an yi masa juyin mulki, ya siffanta masu kitsa zanga-zangar da sojojin haya.