1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tukunyar gas ta fashe a China

March 13, 2024

An samu fashewar tukunyar gas a wani gidan sayar da abinci da ke arewacin kasar China, lamarin da ya kai ga ajalin mutum biyu tare da jikkata mutane 26.

https://p.dw.com/p/4dUAE
Hoto: Iman Baruna/DW

Ma'aikatan agaji sun ce lamarin ya yi munin da ya kai ga kone manyan gine-gine biyu da wata mota da ke kusa da inda al'amarin ya faru.

Mahukunta sun ce sun aiko da motocin kashe gobara 36 dauke da jami'ai 154 wadanda suka yi nasarar kashe wutar da ta balbale wurin dafa abincin. Tuni kamfanin da ke samar da iskar gas a yankin ya sanar da dakatar da tura wa gidaje 50 da ke kusa da gidan cin abinci gas har zwa lokacin da al'amura za su daidaita.

Fashewartukunyar gasirin wannan ba wani sabon abu ba ne a China, inda yawaitar faruwar hakan ta sanya Shugaba Xi Jinping kira ga mutanen kasar da su yi taka-tsan-tsan.