1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Kishi,na saka rayuwar iyali cikin hadari

May 2, 2024

A arewacin Ghana wata kotu ta daure wata ma'aikaciyar jinya hukuncin zaman gidan yari na gyara hali tsawon shekaru shida saboda kona mijinta da ruwan zafi.

https://p.dw.com/p/4fQWl
Hoto: Gregory Bull/AP/picture alliance

 Zeinab Mohammad Ali,uwar yaya biyu ta fada wa kotu cewa ta aikata laifin ne a yunkurin kare kanta. Sai dai kuma bayanan ba su gamsar da alkalin kotun ba, wanda ya zartas da hukuncin. Irin wannan al'amari daya ne daga cikin misalai a Ghana inda bayan samun tashin hankali sautari saboda kishi mata kan dauki mataki a kan mazajensu ta hanyar   jikkatasu.

Kishi dalilin samun yawan rikici a tsakanin ma'aurata a Ghana

Symbolbild Afrika Nigeria Schwangerschaft Gefangenschaft Kriminalität Gewalt an Frauen
Hoto: Shehzad Noorani/AP/picture alliance

Yanzu haka dai mijin wannan mata yana kwance a asibiti yana yin jinya babbar ayyar  tambaya ita ce ko wanne dalili ne ke janyo kiyayya tsakanin ma'aurata a Ghana. Malama Mannara Abdulmumuni, mai ba da shawarwarin aure a gidauniyar nan ta Peace da’awa ta ce yawanci kishi ne na matan kan yawan janyo tashin hankalin da zaran miji ya bayyana aniyarsa na yin   karin aure.