1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sojojin na fama da rashin kayan yaki

May 9, 2024

Masana tsaro da masharhanta da ma wadanda matsalolin suksa shafa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya sun fara tofa albarkacin bakin su bayan da rundunar sojojin Najeriya ta ce tana fama da rashin kayan yaki isassu.

https://p.dw.com/p/4fg8I
Nigerianische Armee | Nigeria
Hoto: AUDU ALI MARTE/AFP/Getty Images

  RundunarSojojin Najeriya ta ce rashin kayan yaki isassu kuma na zamani da karancin da sojoji suka yi na shafar ayyukansu a yakin da suke yi da ta'addanci. Babban Kwamnadn kula da dakarun Infatary Manjo Janar Olufemi Oluyede shi ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a bikin bude makon horo ga dakarun Infantary wanda aka yi a barikin sojoji da ke Jaji a Jihar Kaduna.  Masanatsaro sun ce maganar rashin isassun kayan yaki na zamani da karancin sojoji matsala ce da ta jima da dakushe kokarin yaki da ta'addanci a Najeriya.

Karkatar da kudaden sayen makamai na daga cikin dalilan samun karancin kayan yakin 

Nigerianische Armee | Nigeria
Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Kwararruna ganin na cewa karancin kudi da ake ware wa harkokin tsaron a kasafin kudi na shekara na daga cikin dalilan matsalar da ma karkata wasu kudaden da aka tsara domin sayen makamai,wanda sautari haklan ke faruwa.