1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rahoton wa'adin mulkin shugaban Ghana

February 27, 2024

Shugaba Nana Akufo Addo na Ghana ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki na wa´adin mulkinsa, wanda ke kan turbar kundin tsarin mulkin kasar na gabanin fara sabuwar majalisa, kana kamin warware zaman majalisa.

https://p.dw.com/p/4cx5T
Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana
Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar GhanaHoto: Michael Kappeler/dpa

 

Report

A cikin gabatar da jawabin shugaban kasar ya bayyana nasarori da gwamnatinsa ta cimma tun daga lokacin da ta kama madafun mulkin kasar tun daga kan tattalin arziki da sauran muhimmun bangarori amma ya fara kafa hujja ne da yanayin ingancin tsaro a Ghana, duk da matsalolin ta'addanci da ake fuskanta a wasu kasashe da ke yanki masu makwabtaka da kasar ta Ghana. Shugaban ya ce tilas kasar ta kara zage damtse wajen tabbatar da tsaro.

Karin Bayani: Ghana na fama da karancin kujeru a makarantun firamare

Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana
Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar GhanaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Manazarci kan harkokin gwamnati Abdallah Abdurraheem ya yi tsokaci kan yadda jama'ar kasar ke nuna halin rashin kula bisa irin matsalolin bayanan shugaban kasa da gardamar cewa, yawancin ababan da shugaban kasar ke alfahari da su, ba a gani a kasa. Ghana na fama da masasarar tattalin arziki wanda ya tilasata mata garzawa ga asusun lamu nin kudi na duniya dan agaji.

Shugaban kasar a cikin bayanansa ya ce babu wani kalubalen da Ghana za ta fuskanci a shirin sakamakon sauke ministan kudi. Bangaren adawar gwamnati a farko dai sun so kauracewa zaman daga bisani suka dawo cikin majalisar bayan tsohon shugaban kasa ya gana da su. Mohammad Nazeer na daga cikin jami'an sadarwar jam'iyyar NDC wanda ya yi bayani kan bayanan shugaban kasar. A cikin wadanda suka hallara dai an samu tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama, da ministoci, jakadu, sarakuna muhimmun masu fada a ji a Ghana.