1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP ta ce babu batun karba-karba a 2023

Uwais Abubakar Idris MAB
March 18, 2021

A wani muhimmin mataki na fitar da dan takarar neman shugaban kasa, jam'iyyar adawa ta PDP ta kama hanyar watsi da tsarin karba-karba domin sakar wa kowa marar fafatawa don neman kujerar mulkin kasar a zaben 2023.

https://p.dw.com/p/3qp4B
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Babbar jam'iyyar adawar Najeriyar ta PDP ta dago da wannan batu ne a daidai lokacin da jam'iyyun siyasar kasar ke fara shiri na zaben 2023 da ke tafe a kasar. Kwamitin da jam'iyyar ta kafa da ya yi nazarin yadda aka gudanar da zaben shugaban Najeriyar na 2019 inda daya daga cikin batutuwan da aka gabatar ya nemi jam'iyyar ta yi watsi da batun karba-karba don baje neman dan takarar a faifai ga kowa.


Duk da cewa tsarin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, amma tun 1999 da aka sake maido da mulkin farar hula  jam'iyyun siyasa da dama suke amfani da shi, abin da kwararu a siyasar Najeriya ke cewa ya saba wa tsari na dimukaradiyya. Duk da cewa ana daga murya a tsakanin sassan Najeriya da ke cikin jam'iyyar domin neman a ba su ikon samar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, lamarin da zai haifar da ci gaba a tsarin jam'iyyar ta PDP. 

Nigeria Benin City | Edo State Wahlen | Godwin Obaseki gewinnt
PDP ta yi murna lokacin da ta ci zabe a jihar Edo 0 2020Hoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa


A yayin da wannan ke faruwa ga jam'iyyar APC mai mulki na bayyana duk wani mataki ba zai razanata ba. Abin jira a ganin shi ne ko wannan zai taimaka ragewa ko kawar da siyasar ubangida da masana kimiyar siyasa ke dangata shi da daya daga cikin matsalolin da ke sanya yi wa jama’a karfa-karfa maimakon zaban wakilai sahihai a kasar.