1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisa ta yi watsi da bashin sayen gidan sauro

Uwais Abubakar Idris
October 28, 2021

A Najeriya bukatar da gwamnatin kasar ta gabatar na neman amincewar majalisar datawa ta amince mata karbo bashin dalla milyan 200 domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro ya gamu da cikas

https://p.dw.com/p/42Jhm
Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Ci gaba da karbo basussukan da gwamnatin Najeriyar ke yi ya fara kai wa ‘yan majalisa wuya, bisa ga yadda suka dage a wannan karon suka nuna basu yarda da bukata da ma’aikatar kula da harkokin lafiya ta Najeriyar ta gabatar mata don karbo bashin dala milyan $200 domin shigo da gidan sauron da aka yiwa feshin magani ba, sannan wani kuma a samar da shi a cikin Najeriyar a karkashin shirin yaki da zazzabin malaria. 

Ita dai ma’aikatar lafiyar ta dage cewa za ta yi amfani da bashin ne domin yakar cizon sauro a jihohin Najeriya 13 da kananan hukumomi 208 da suka fi fama da zazzabin cizon sauro, ta hanyar samawa jama’a gidan sauron da aka yiwa feshin magani.

To sai dai wannan ya fusata Sanata Ibrahim Oloregbe wanda yace bayan an sanya Naira milyan 450 a kasafin kudi shekara mai zuwa me ya kawo batun bashi a yanzu. 

A baya dai ana wa majalisar dokokin kallon wacce duk wata bukata musamman ta bashi da shugaban kasar ya gabatar sukan amince da ita, ko yaya ake kalon wannan mataki da suka dauka a matakin kwamiti mai kula da karbo basussuka a cikin Najeriyar da kasashen waje?

Ko kafin wannan dai sai da kwamitin ya dakile bukatar karbo bashi na dala milyan $700 da shugaban Najeriyar ya gabatar don samar da ruwa a yankunan karkkara.

Za dai a sa ido a ga ko ‘yan majalisar za su iya rike wuta a kan batun karbo bashin da a yanzu ke sanya Najeriyar biya kudin ruwa mai yawa da ya fara kai wa kasar iya wuya..