1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Fargabar tsaro yayin bukukuwan Sallah

April 8, 2024

Matafiya musamman masu zuwa bukukuwan Sallah na nuna damuwa bayan wani harin kwantar Bauna da aka yi wa sojojin Najeriya a hanyar Biu zuwa Damaturu ya kai ga mutuwar sojoji shida.

https://p.dw.com/p/4eYIE
Tsaro a lokacin bukukuwan Sallah
Tsaro a lokacin bukukuwan SallahHoto: Munir Uz Zaman/AFP

A dai dai lokacin da al'ummar musulmi ke shirin shagulgulan Sallar Eid-El-Fitr a karshen azumin watan Ramadan, matafiya na bayyana fargaba na bin wasu hanyoyi saboda matsalolin tsaro.

Harin kwantar bauna da aka kai wa tawagar Sojoji a kan hanyar Biu zuwa Buni wacce ke bullewa har Damaturu na cikin abun da ya tada hankulan matafiya a wannan sashi na Najeriya.

Sojojin sun gamu da ajalinsu ne bayan da mayakan Boko Haram suka bude musu wuta a kauyen Kumuya da ke kusa da Kauyen Buratai a jihar Borno yayin da suke kan hanyar zuwa Damaturu domin nemo Man Fetur.

Sintirin sojoji a arewa maso gabashin Najeriya
Sintirin sojoji a arewa maso gabashin NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da wannan hari da ma kisan da aka yi wa jami'inta inda ta ce ta hallaka wasu mayakan da suka yi wannan kwantar Bauna.

Wannan yanayi ya jefa tsoro a zukatan yawancin matafiya a wannan lokacin kamar yadda Malam Muhammad Naziru ya bayyana.

"Ba shakka ina so in je Sallah amma to ina tsoro, gaskiya ina tsoron hanyar matuka saboda tun can ma hanyar ga yadda ta ke ana lallabawa ne.”

Malam Mamman Umar Kida da mayakan Boko Haram suka taba tarewa a hanyar Biu zuwa Buni Yadi ya ce lamarin tsaro a wadannan hanyoyi abun tsoro ne.

"Muna tafiya da mata ta da ‘ya‘yana da Kanina da matarsa muna tafiya sai kawai ga Boko Haram sun fito. Da farko mun dauka ‘yan banga ne mun ga kawai an ajiye itace a kan hanya direban mu ya tsaya za mu cire itacen kawai sai muka ga sun fito mana sun kai su bakwai, hudu akan Mashin guda uku kuma suna tsaye hakan nan sai suka kewaye mu suka tambaye mu daga ina kuke, direban mu yayi sauri yace daga Damaturu muke. Suka tambaye ni kai me ye sana'ar ka, sai nace ina aikin hannu ne suka kale mu sai suka ce maza mu juya, mu je mu cewa Sojoji an tare mu an ce mu koma.”

Sojin Najeriya cikin shirin ko ta kwana
Sojin Najeriya cikin shirin ko ta kwanaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Direbobi da wadanda ke bin wadannan hanyoyi sun yi kira ga jami'an tsaro su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a hanyoyin.

Sale Bakuro Baraden Tikau daya daga cikin shugabannin Kungiyoyin direbobi ne a jihar Yobe.

"Ya kamata jami'an tsaro su zage damtse wajen kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu. Musamman mu da muke garin Damatutru akwai hanya da ta tashi daga Damaturu zuwa Biu har su Gombi da sauran ya kamata a ma ko ina a Najeriya jami'an tsaro su zage Damtse a ga cewa an yi Sallah karama lafiya.”

To sai dai rundunar Sojojin Najeriya ta dauki matakai na tabbatar da tsaro inda aka shaida ganin karin sintiri na jami'an tsaro a yawancin hanyoyin da ma sassan jihohin arewa maso gabashin Najeriyar.