1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Barazanar 'yan siyasa ga tasirin kotuna

August 31, 2021

A kokarin ceto tsarin shari'ar Najeriya daga sabuwar barazana ta 'yan siyasa, babban alkalin kasar ya aike da sammaci ga wasu manyan alkalan jihohi kan wasu shari'u dake neman hargitsa harkokin jam'iyyun kasar

https://p.dw.com/p/3zkIE
Nigeria National Assembly
Hoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Wasu umarni na kotuna a jihohi daban daban na neman hargitsa lamura a cikin manyan jam'iyyu biyu na PDP da yar uwarta ta APGA a Najeriya

Umarnin kotun Jihar Rivers da yar uwarta ta Kebbi dai alal ga misali ya haifar da shugabanni guda biyu cikin jam'iyyar PDP ta adawa a yayin kuma da can a Jigawa kotun ta tsallaka kusan kilomita 1000 ta kuma nemi tabbatar da ko wanene zai zama dan takara ga jam'iyyar APGA a zaben gwamnan jihar Anambra.

Abun kuma da ya tada hankalin babban alkalin kasar da ya aika sammaci da nufin neman bin ba'asin yadda alkalan suka nemi komawa 'yan kore na siyasa.

Nigeria National Assembly
Hoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Ana sa ran manyan alkalan a jihohin Kebbi da Rivers da Imo da Jigawa da Cross Rivers ko bayan jihar Anambra za su bayyana gaban majalisar alkalai ta kasar kila da nufin tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.

To sai dai kuma tuni badakalar da ake yiwa kallon na iya tasiri ga zabbukan da ke tafe da ma makomar dimukuradiyyar kasar da ya fara daukar hankali cikin jam'iyyu da masu ruwa da tsaki da neman ingantar tsarin dimukuradiyyar kasar.

Sanata Umar Tsauri na zaman sakataren jam'iyyar PDP na kasa da kuma shari'ar ta kaita tangal tangal zuwa yanzu. Kuma a fadarsa abun da ke faruwa a kotunan kasar na zaman tsohuwar al'ada a siyasar kasar.

Nigeria National Assembly
Hoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Ihu bayan hari ko kuma kokari na siyasa da batun shari'ar dai, sabon rikicin na kara fitowa fili da irin girman barazanar da kasar ke iya fuskanta ga tarrayar Najeriyar da ke dada fuskantar zabe. Abun kuma da a cewar Dr Faruk BB Faruk da ke sharhi kan harkar siyasa ya sanya ake da bukatar dauke shari'un siyasa daga kotunan da ke daure Awaki da Rakuma cikin kasar.

Dimukuradiyya 'yanci ko dimukuradiyya ta tuwo dai, tsarin shari'ar kasar alal misali ya haramta kotuna guda biyu masu iko iri daya yanke hukunci akan batu guda.

Barrister Buhari Yusuf wani lauya mai zaman kansa a Abuja yace barazanar ta dara fagen siyasa ta kuma doshi daukacin kasar da ke kallon shari'ar a matsayin fatan karshe ga kowa.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin babban alkalin wajen iya taka birki da zai kai karshen annobar da ke zama mai hatsari ga makomar kasar.