1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Wakilan Amirka ta amince da rufe TikTok

March 14, 2024

Shugabannin kamfanin TikTok sun musanta alakarsu da kasar China, suna masu rokon sanatocin Amurka su yi wa kudurin rufe manhajar karatun ta-natsu sabanin hanzarin da 'yna majalsiar wakilai suka yi.

https://p.dw.com/p/4dU9u
Hoto: Marijan Murat/dpa/picture alliance

Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudurin da zai kai ga toshe shafin sada zumunta na Tiktok a kasar gaba daya. 'Yan majalisa 352 sun bai wa kamfanin mallakin kasar China watanni shida wa'adin ko dai ya sayar da TikTok ga Amurka ko kuma su toshe amfani da shi a kasar gaba daya.

 Sai dai a yayin da kudurin hana TikTok din ya yi gaggawar wucewa a Majalsiar Wakilai, ana fargabar Majalsiar Dattawan kasar ka iya kin amincewa da yunkurin rufe TikTok din. To amma Fadar mulki ta White House ta ce Shugaba Joe Bidena shirye yake ya rattaba hannu a kan kudurin madamar majalisun kasra biyu suka amince da shi.