1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ibrahimovic ya bar sana'ar taka leda

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
June 5, 2023

Zlatan Ibrahimovic na Ac Milan ya bar wasan kwallon kafa kwata-kwata yayin da Karim Benzema ya yi sallama da Kungiyar Real Madrid.

https://p.dw.com/p/4SCrN
Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga sana'ar taka leda
Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga sana'ar taka ledaHoto: Antonio Calanni/AP Photo/picture alliance/dpa

Kungiyar USM Alger ta lashe kofin Confederation cup na Afirka duk da diban kashinta a hannu a ci 0-1 da ta yi a hannun Young Africans ta Tanzaniya a mataki na biyu na wasan karshe. Wakiliyar ta Aljeriya duk da ta samu wannan damar ne sakamakon nasarar da ta yi a wasan farko da ci 2-1. Wannan shi ne karon farko da wata kungiya ta kwallon kafar Aljeriya ta lashe irin wannan kofi na Afirka, lamarin da ya kawo karshen babakere da abokiyar gabarta Maroko ta saba yi a wannan fanni. Sai dai duk da sanya sunanta a kundin Aljeriya da Afrika da ta yi, a yanzu dai USM Alger na a matsayi na 10 kacal a babban lig na kwallon kafar Aljeriya.

Yan wasan Kungiyar USM Alger
Yan wasan Kungiyar USM AlgerHoto: Sports Inc/empics/picture alliance

A fannin gasar cin kofin zakarun Turai kuwa a karawar matakin farko na wasan karshe da ya gudana a birnin Alkahira, Al Ahly ta Masar ta doke Wydad Casablanca mai rike da kofin gasar da ci 2-1. Sai dai wakiliyar Maroko ta cika baki game da zagaye na biyu na wasan, inda ta sha alwashin mamaye Al-Ahly tare da lashe kofin na Champons lig karo na biyu a jere. Amma dai sau 14 ne Kungiyar Al Ahly ta taba lashe kofin zakarun Afirka, kuma a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni ne za a san maci tuwo tsakanin kungiyoyi biyu da ke fada a ji fagen tamaular nahiyar Afirka, a fafatawa da za a yi a filin wasa na Mohammed V da ke Casablanca.

A daidai lokacin da ya rage kwanaki biyar a gudanar da wasan karshe na kofin kwallon kafa na zakarun Turai tsakanin Manchester City  da Inter Milan a filin wasa na Atatürk da ke Istanbul, kungiyar mata ta Barcelona ta lashe kofin Champions league a gaban takwarta ta Wolfsburg a birnin Eindhoven na kasar Netherlands. Amma dai 'yan matan Wolfsburg ne suka fara zura wa kwallaye biyu a ragar 'yan wasan FC Barcelona, kafin 'yan matan na Spain sun mayar da martani inda suka zura kwallaye uku a karawar da ke zama ta biyu, kuma aka tashi ci 3-2. Wannan ita ce nasara ta biyu da kungiyar Barça ta mata ta samu a wannan gasa bayan kofin da ta lashe a 2021 tare da zama daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na mata da suka fi taka rawar gani a nahiyar Turai.

A nan Jamus kuwa, an gudanar da wasan karshe na neman cin kofin kalubale na kwallon kafar kasar a yammacin ranar Asabar, inda  shekara ta biyu a jere, RB Leipzig ta yi nasara, a wannan karon a kan Frankfurt da ci 2-0. Christopher Nkunku ne ya zura kwallon farko a minti na 71 da fara wasa yayin da Dominik Szoboboskai ya ci na biyu mintuna kalilan kafin a yi busan karshe. Wannan kofi na biyu da RB Leipzig ta samu a cikin shekaru biyu ya ba ta damar samun kwakkwaran matsayi a fagen kwallon kafa na Jamus, bisa taimako da hamdalar kocinta Marco Rose, wanda dan asalin birnin ne.

Yan Wasan RB Leipzig bayan lashe kofin kalubale na DFB
Yan Wasan RB Leipzig bayan lashe kofin kalubale na DFBHoto: Annegret Hilse/REUTERS

Sai dai Frankfurt da ta sha kashi a wasan na karshe, za ta raba gari da kocinta Oliver Glasner a karshen watan, duk da matsayin na 7 da ta samu a babban lig na Bundesliga, lamarin da ya ba ta damar shiga gasar cin kofin Europa League.

A Ingila kuwa, Manchester City ta lashe kofin kwallon kafa da ake wa lakabi da FA bayan da ta doke makwabciyarta United da ci 2-1 a Wembley. Godiya ta tabbata ga Ilkay Gündogan da ya ci kwallaye biyu, lamarin da ke kwarin gwiwa da 'yan wasan Pep guardiola , 'yan kwanaki kafin wasan karshe na gasar zakarun Turai.  Wannan nasarar ta zo ne kwanaki goma bayan da Manchester City ta zama zakarar kwallon kafar Premier League.

A gasar kwallon kafa ta duniya ta 'yan kasa da 20 da haihuwa da ke gudana a Ajentina, kasar Uruguay ta yi nasarar hayewa wasan kusa da na karshe na neman cin wannan kofi bayan da ta lallasa Amirka da ci 2-0. Ita ma Isra'ila ta kai labari bayan da ta yi wajen road da Brazil bayan da ta doke ta da ci 3-2. A nata bangaren Italiya ta mamaye Kolombiya da ci 3-1, yayin da Koriya ta Kudu ta kawo karshen mafarkin Fying eagles ta Najeriya ta hanyar doke ta da ci 1-0. Wannan dai ya saba da alwashin da kocin Najeriya Ladan Bosso ya sha na kai wasan karshe tare da cin kofin na 'yan kasa da 20 da haihuwa, lamarin da ya masharhanta da magoya baya a Najeriya tofa albarkacin bakinsu dangane da rawar da Flying Eagles ta taka a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru ishirin. 

Dan wasan gaba na kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic mai shekaru 41 da haihuwa ya sanar da kawo karshen wasan kwallon kafa a matsayin sana'a, inda ya shaidawa magoya bayan AC Milan cewa lokaci ya yi da zai yi bankwana da tamaula. Ibrahimovic ya yi wannan shelar ne a filin wasa na San Siro, bayan nasarar da kungiyarsa ta samu a kan Hellas Verona (3-1) a mako na 38 kuma na karshe na babban lig din Italiya. Dama dai ya koma AC Milana karshen 2019 kuma ya ba da gudummawa sosai wajen dawo mata da martabarta, inda ta zama zakaran Italiya a 2022. Amma raunin da ya samu ya hana masa rawar gaban hantsi,  inda ya dawo  taka leda a watan Fabrairu bayan da aka yi masa tiyata a gwiwar hagu a watan Mayun 2022. A yanzu dai Zlatan Ibrahimovic ya zama dan wasan mai yawan shekaru da ya fi kowa zura kwallo a raga a tarihin Seria A.

Karim Benzema a gaban dan wasan Chelsea Thiago Silva
Karim Benzema a gaban dan wasan Chelsea Thiago SilvaHoto: Jose Breton/Manu Fernandez/AP Photo/picture alliance

Dan Kwallon kafar Faransa da ya taba samun Ballon d'Or Karim Benzema zai bar Real Madrid a karshen kakar wasa ta bana, bayan ya shafe shekaru 14 a kungiyar tab babban birnin Spain,  Shugabannin Real da kansu ne suka yi wannan sanarwa 'yan sa'o'i kadan kafin wasan karshe na kakar wasanni Spain, inda suka ce ba za su taba mantawa da kwazonsa a kungiyarsu, ba. Shi dai Benzema mai shekaru 35 da haihuwa ya shafe shekaru 14 a Real Madrid, inda ya taimaka ta ci kofin zakarun Turai biyar. Shi dai mai goya lamba tara, ya kasance na biyu wanda ya fi zura kwallaye a tarihin kulob din Madrid tare da kwallaye 353. Ya dade a inuwar Cristiano Ronaldo a lokacin da ya ke Madrid kafin ya karbi ragamar wasan na Real bayan da dan Portugal din ya tafi a cikin 2018.