1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun Kolin Senegal ta daure madugun adawa Ousmane Sonko

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 5, 2024

Ko da yake Sonko na iya tsallake wannan tarnaki la'akari da hukuncin da Kotun kundin tsarin mulkin kasar za ta yanke anjima a juma'ar nan

https://p.dw.com/p/4asVS
Hoto: Seyllou/AFP

Kotun Kolin Senegal ta jaddada hukuncin daurin watanni 6 da aka yanke wa madugun adawar kasar Ousmane Sonko, lamarin da zai haramta masa shiga zaben shugaban kasa, bayan samunsa da laifin bata sunan ministan yawon bude idon kasar Mame Mbaye Niang.

Karin bayani:Sénégal: An hana gangamin siyasar da zai tsayar da Sonko takara

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito lauyan gwamnati El Hadji Diouf na tabbatar da hukuncin da alkalin kotun Kolin kasar Abdourahmane Diouf ya yanke a cikin daren Alhamis zuwa Juma'a, tare da tarar kudi CFA miliyan 200.

Karin bayani:'Yan adawar Senegal sun tsayar da Sonko

Ko da yake Sonko na iya tsallake wannan tarnaki la'akari da hukuncin da Kotun kundin tsarin mulkin kasar za ta yanke anjima a juma'ar nan.