1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kasashen Larabawa sun bukaci a kawo karshen yakin Gaza

May 16, 2024

Kasashen Larabawa sun kammala taro a birnin Manama na kasar Baharein inda suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki mataki na kawo karshen yakin Gaza da ke ci gaba da lakume rayukan Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/4fxOm
Kasashen Larabawa sun bukaci a kawo karshen yakin Gaza
Kasashen Larabawa sun bukaci a kawo karshen yakin GazaHoto: Qatar Amiri Diwan/Handout/Anadolu/picture alliance

Kungiyar kasashen Larabawa ta bukaci da a kai jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dindin Duniya zuwa yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye, kafin a cimma daidaito na kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci.

Sai dai da akwai wuya wannan kira ya yi tasiri, duba da sarkakiyar rikicin da aka share shekaru ana yi a wannan yanki.

Karin bayani: G20 ta amince da samar da kasar Falasdinu

A cikin sanarwar da ta biyo bayan taron da aka kammala a ranar Alhamis, shugabannin kasashen Larabawan sun bukaci a shirya babbar mahawara ta kasa da kasa a karkashin inuwar Majalisar Dindin Duniya domin kawo karshen zubar da jini a zirin Gaza da yaki ya daidaita.

Karin bayani: Majalisar Dinkin Duniya ta ce samar da kasar Falasdinu ya zama wajibi

Sai dai girke jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD a yankin Falasdinu abu ne da ke bukatar samun sahalewa daga Isra'ila, abinda wasu masana ke ganin cewa zai yi matukar wahala ko ma ba zai yiwu ba.

A daya bangaren kuma firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya kasance babban mai adawa da matakin kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci a matsayin mafita ga rikicin yankin, duk da karbuwa da wannan shawara ke samu a gurin Amurka da wasu kasashen nahiyar Turai.