Kanada ta janye halascin shan miyagun kwayoyi
April 27, 2024Gwamnatin lardin British Columbia ita ce ta dakatar da dokar kamar yadda Firimiyan yankin David Eby, ya sanar a shafinsa na X, ya ce jami'an 'yan sanda zasu ci gaba da aikin kakkabe masu ta'ammali da kwayoyin a wuraren taruwar jama'a ciki har da asibitoci da wuraren cin abin abinci da bakin ruwa harma da wuraren shakatawar jama'a.
Karin bayani: Mutum na karshe na harin Kanada ya mutu
Firimiyan ya kara da cewa wannan mataki ya kawo karshen dokar da ake ta cece-kuce a kai daga ciki da wajen kasar, wanda tun da fari ta bawa al'umma damar amfani da miyagun kwayoyin a bainar jama'a da suka hadar da hodar iblis da heroin da dai sauransu.
Karin bayani: Kanada ta hana 'yan Afirka zuwa taron HIV/AIDS a kasarta
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakiyar kwamishiniyar 'yan sandan Vancouver, Fiona Wilson, ta bayyana wa zauren majalisar dokoki cewa 'yan sanda basu da hurumin hana mutane shan kwaya, matsala ce da ta shafi bangaren kiwon lafiya da hukumomi ya kamata su tashi tsaye.