1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHaiti

Jagororin Haiti sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 9, 2024

Jagororin sun tsara bai wa gwamnatin rikon kwaryar wa'adin shirya zaben shugaban kasa sannan ta mika ragamar mulkin a ranar 7 ga watan Fabarairun shekarar 2026

https://p.dw.com/p/4eZ6o
Hoto: Ralph Tedy Erol/REUTERS

Jagororin siyasar kasar Haiti mai fama da rikici sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar da ke yankin Caribbean, to amma suna jiran sahalewar gwamnati mai barin gado kan kudurin.

Karin bayani:'Yan Kenya na adawa da matakin gwamnatin na tura 'yan sanda a Haiti

A wasikar da suka aikewa kungiyar raya kasashen Caribbean, jagororin sun tsara bai wa gwamnatin rikon kwaryar wa'adin shirya zaben shugaban kasa sannan ta mika ragamar mulkin a ranar 7 ga watan Fabarairun shekarar 2026.

Karin bayani:Firaministan Haiti ya yi murabus daga mukaminsa

Haka zalika a cikin yarjejeniyar, babu wanda zai tsaya takara a cikin mambobin gwamnatin rikon kwaryar.

A ranar 11 ga watan Maris din da ya gabata ne firaministan Haiti Ariel Henry ya yi murabus, bayan da 'yan daba masu gwagwarmaya da makamai suka kwace iko da babban birnin kasar Port-au-Prince, inda suka kai hari filin jirgin sama da tashar ruwa, da kuma balle gidajen yari tare da sakin dubban daurarru.