1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Finidi ya zama sabon mai horar da Super Eagles

Aliyu Muhammad Waziri
May 1, 2024

Masharhanta lamuran wasanni musamman kwallon kafa a Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayinsu game da nadin sabon mai horas da Super Eagles da hukumar NFF ta yi na Finidi George

https://p.dw.com/p/4fP04
Nigeria Super Eagles Neu Trainer Georges Finidi
Hoto: Nigerian National Football Federation

Nadin Finidi George da hukumar kwallon kafar Najeriyar ta yi ya zo wa jama'a da matukar mamaki, lura da cewa ba ya cikin jerin mutane biyar da ake ganin su ne kan gaba wajen samun matsayin, sai ga shi kwatsam NFF ta ayyana sunansa a matsayin wanda zai jagoranci tawagar ta Super Eagles a wannan gaba musamman ma da yake yana daga cikin mataimakan tsohon mai horas da 'yan wasan Najeriyar Jose Peseiro da suka raba gari bayan kammala gasar cin kofin kasashen Afirka da aka kammala a bana. Dalili kenan ma da yasa Imrana Yakubu na kungiyar marubuta labarin wasanni SWAN yake ganin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa ta Najeriya ba da gaske suke ba wajen kawo gyara.

Karin Baya: Najeriya za ta yi rawar gani a gasar cin kofin Afirka

Sabon mai horar da Super Eagles Finidi George
Sabon mai horar da Super Eagles Finidi GeorgeHoto: Nigerian National Football Federation

Tun kafin a kai ga sanarwar nadin, Emmanuel Amanuke wanda shi ma tsohon dan wasan Super Eagles ne shi ne ake gani a sahun gaba da ake sa ran zai samu matsayin baya ga wasu daga kasashen ketare da suke biye da shi, duk da cewa kokarin sake nada wani daga wajen ya gamu da suka daga masana da ma 'yan wasan kasar, shi yasa duk hankalin akasarin masharhanta ya karkata cewa na gida za a dauka wanda kuma hakan ne ya faru amma ba ta inda aka yi tsammani ba.

Karin Bayani: Wace kasa ce ke da karfin lashe kofin AFCON a 2024?

Sabon mai horar da Super Eagles Finidi George
Sabon mai horar da Super Eagles Finidi GeorgeHoto: Nigerian National Football Federation

Ganin cewa mai daki shi ya san inda yake masa yoyo kuma da dan gari a kan ci gari yasa shi a tasa fahimtar Sadiq Disina ke ganin akwai dumbin hikima tattare da nadin Finidi George a matsayin sabon mai horas da Super Eagles din domin kuwa idan har ba a bada dama ga irin sa, to tabbas nan gaba ba za ma a dubi na cikin gidan ba, sai dai a yi ta nemo wasu daga waje wanda kuma ba zai taba zama mafita ga makomar kungiyar ta Super Eagles ba. Yanzu babbar jarabawar da Finidi George zai fuskanta ita ce neman gurbi ga Najeriya a gasar cin kofin kasashen Afirka da ta duniya a shekarar 2026