1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Biden da Trump sun yi fintinkau a "Super Tuesday"

March 6, 2024

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da mai ci yanzu Joe Biden sun samu gagarumar nasara a zaben da ake yiwa lakabi da "Super Tuesday " Wanda ya kunshi jihohi 16 da kuma gunduma daya.

https://p.dw.com/p/4dD1z
Joe Biden da Donald Trump a neman shiga White House
Joe Biden da Donald Trump a neman shiga White HouseHoto: ABACA/IMAGO;AP Photo/picture alliance

 Wannan zabe na 'Super Tuesday' zai ba da damar yakin karshe tsakanin tsohon shugaba Trump da shugaba Mai ci Biden a zaben shugaban kasa na 7 watan Nuwamban 2024.

Karin bayani:Kotun Illinois ta cire sunan Donald Trump daga cikin zaben fitar da gwani takarar shugaban kasa

A jawabin da ya gabatar gaban dandazon magoya bayansa a harabar gidansa da ke Florida, Mr. Trump na jam'iyyar Republican ya bayyana ranar a matsayin daren alkhairi mai cike da ban al'ajabi. Trump ya kuma soki Biden kan manufofinsa da suka shafi shige da fice a iyakar Mexico, inda ya bayyana su a matsayin aikin 'Baban giwa".

Karin bayani:Donald Trump da Hillary Clinton sun yi nasara

Kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito cewa Nikki Haley da ke kasancewa 'yar takara daya tilo da ke hamayya da Trump a zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican ta yi nasara a jihar Vermont.