1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da tallafin abinci ga Habasha

June 10, 2023

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da aniyar dakatar da bayar da tallafi ga Habasha sakamakon karkata akalar abincin da ake ba wa kasar.

https://p.dw.com/p/4SPjf
A sansanin 'yan gudun hijirar irin wannan aka fi raba abinciHoto: MAHAMAT RAMADANE/REUTERS

A cikin sanarwar da ta fidda, hukumar ta ce matakin bai shafi tallafin da ta saba bayarwa a fannin yaki da tamowa, da kuma wanda take ba wa mata masu juna biyu da dalibai da kuma manoma da makiyaya ba. Sai dai dakatar da tallafin abinci  na zuwa a daidai lokacin da Amirka ta dauki makamancin wannan mataki bisa la'akari da rashin isar tallafin abincin ga 'yan Habasha da ake yi domin su.

Kai tsaye dakatar da tallafin zai shafi sama da mutane miliyan 20 wato kusan kashi 16% na al'ummar kasar ta Habasha da ke fama da bala'in yunwa sakamakon yake-yake da fari mafi muni da ake ake fama da shi a kasashen da ke kahon Afrika, wanda ya tilasta wa kusan mutane miliyan biyar tserewa izuwa waje baya ga sabbin 'yan gudun hijirar Sudan da yawan su ya haura mutane dubu 30.