1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An binne gawa 85 a kauyen Tudun Biri

December 5, 2023

Adadin wadanda suka mutu a harin da jirgi marasa matuki ya kai a wani kauyen da ke cikin Jihar Kaduna Najeriya wato Tudun Biri na karuwa.

https://p.dw.com/p/4ZorN
Wasu da suka ketare rijiya da baya a harin
Wasu da suka ketare rijiya da baya a harinHoto: AP

 Wani jirgi mara matuki na sojojin Najeriya ya halaka akalla fararen hula 85 a ranar Lahadin da ta gabata a wani kauye da ke Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, a wani harin  bama-bamai da sojoji suka kai a kasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da bincike

Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike a bayan da rundunar sojin kasar ta amince da cewa daya daga cikin jiragenta da ke kai hari kan kungiyoyin da ke dauke da makamai ya afkawa kauyen  Tudun Biri bisa kuskure, wanda mazaunansa ke gudanar da bukukuwan Musulmi na Maulidi. Rundunar sojin kasar dai ba ta bayar da alkaluman adadin wadanda suka mutu ba, amma mazauna yankin sun ce mutane 85 da yawancinsu mata da yara ne aka kashe. “Ofishin shiyyar Arewa maso aymma ya samu labari daga hukumomin yankin cewa kawo yanzu an binne  gawarwaki 85,yayin da ake ci gaba da bincike. Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, mai tayar da hankali da raɗaɗi, ya kuma bayyana takaicinsa da alhininsa game da mummunan asarar rayukan da aka yi a Nijeriya ya kuma bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da fadar  shugaban kasar ta bayyana.