1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na fama da karancin malamai

December 5, 2023

Amirka na fuskantar matsalar karancin malaman makarantun boko adai-dai lokacin da ake shirye-shiryen shiga sabuwar shekarar karatu a shekarar 2024.

https://p.dw.com/p/4ZnhW
Weltspiegel | USA Präsident Joe Biden Bildungsreform
Hoto: Mandel Ngan/Getty Images/AFP

.A cikin wani rahoto da cibiyar kididdiga da kuma nazarin makaratun gwannati ta kasa ta fitar, ta ce a halin yanzu kashi 86 cikin dari na makarantun suna da karancin malamai. Bayan duba wasu makarantun firamare zuwa na babbar Sakandare fiye da dubu daya da 300 a fadin kasa, cibiyar ta gano cewa, tara cikin 10 na makaratun gwamnati, suna neman malamai wurjajan; musanman a darussan kimiyya, da na koyar da  harsunan ketare.

Dalilan karancin malaman a Amurka ya fara bayan annobar corona

Karancin malaman makaranta a Amirka
Karancin malaman makaranta a AmirkaHoto: Eric Seals/AP Photo/picture alliance

Wasu majiyoyi suna cewa, akwai makaratun da a yanzu suke yin karatun kwana hudu cikin sati a maimakon biyar, saboda karancin malamai. Babban dalilin baya-baya da ya haddasa wannan matsala, shi ne, rayukan da aka rasa a lokacin annobar corona, da sabawa da yin aiki daga gida, don haka, wasu malaman, suka gwammace su bar aikin.Bukatar agajin gagawa ga al'umma zai karu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani